in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya yi kira da a karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa
2017-09-05 13:24:26 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga shugabannin kasashen da ke samun saurin ci gaba, da su dauki matakan fadada hadin gwiwa da mu'amala tsakaninsu da kasashe masu tasowa.

Shugaban na Sin wanda ya yi wannan tsokaci a Talatar nan, yayin taron muhawara tsakanin jagororin kasashe masu saurin ci gaba da na kasashe masu tasowa, zaman da bangare ne na taro na 9 na shugabannin kasashe mambobin kungiyar BRICS, wanda ke gudana a birnin Xiamen na nan kasar Sin. Ya ce sassan kasashe masu saurin ci gaba da masu tasowa na da makamantan kudurorin samun ci gaba.

Shugaba Xi ya kara da cewa, zurfafa hadin gwiwa tsakanin wadannan sassa zai haifar da tarin alfanu, matakin da zai samar da cin gajiya ga juna. Ya ce an gayyaci wakilai daga kasashe masu tasowa daga sassa daban daban na duniya, domin a fadada hade sassan duniya, ta yadda hadin gwiwa da mu'amala za ta karu, matakin da zai kai ga samar da ci gaba da nasarorin da aka sanya gaba, da buri na bai daya tsakanin sassan duniya.

Shugaba Xi ya kuma bayyana alkawarin kasar Sin na samar da kudi da yawansu zai kai dalar Amurka miliyan 500, domin tallafawa kudurorin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa.

Baya ga shugabannin kasashen Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin, da Afirka ta kudu wadanda su ne mambobin kungiyar ta BRICS, taron na bana ya kuma samu halartar shugabanni daga kasashen Masar, da Guinea, da Mexico, da Tajikistan da kuma Thailand. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China