Haidar al-Abadi ya kara da cewa, Iraqi ta yanke shawarar gabatar da wani kuduri na yaki da ta'addanci ga kwamitin sullhu na MDD.
Firaministan wanda ya bayyana haka a jiya yayin wani taron manema labarai da ya kan yi bayan kammala taron majalisar zartaswa na mako-mako, ya ce kudurin na da nufin kawo karshen ta'addanci da kuma wadanda ke da alaka da kungiyar IS, saboda 'yan ta'addan za su sake komawa wasu yankuna su bada kama.
Har ila yau, Ministan ya ce akwai bukatar bibiyar hanyoyin da kungiyar IS ke bada horo da kuma samun kudi. (Fa'iza Mustapha)