Yau Talata 22 ga wata, James Mattis, ministan tsaron kasar Amurka ya kai wata ziyarar ba-zata a kasar Iraki, inda zai yi shawarwari da firaministan Iraki Haider al-Abad, da takwaransa na Iraki da sauran jami'an kasar, dangane da sabon ci gaba da aka samu a yaki da 'yan tawayen IS, musamman ma yakin da ake fafatawa na maido da Tal Afar zuwa hannun gwamnatin Iraki. (Tasallah Yuan)