in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ce tashin hankalin Iraqi ya yi sanadiyyar hallaka fararen hula 239 a watan Yuli
2017-08-02 10:23:23 cri
Shirin tallafi na MDD a kasar Iraqi (UNAMI) ya sanar da cewa, matsalar tashin hankali, da ayyukan 'yan ta'adda da na masu dauke da makamai a duk fadin kasar Iraqi ya yi sanadiyyar hallaka fararen hula kimanin 239, kana wasu 273 kuma sun samu raunuka a cikin watan Yuli kadai.

Mafi yawan hasarar rayukan ya faru ne a arewacin lardin Nineveh, inda aka kashe mutane 121, mutane 112 kuma suka samu raunuka a lokacin da aka gwabza tsakanin dakarun sojin Iraqi da masu fafutukar kafa daukar musulunci (IS) da 'yan ta da kayar baya na yammacin birnin Mosul.

Jan Kubis, jakadan MDD a Iraq kuma babban jami'in UNAMI, ya yi Allah wadai da ayyukan ta'addanci da mayakan kungiyar IS suka kaddamar, wanda ya yi sanadiyyar jefa rayuwar fararen hula cikin matsanancin hali wadanda suka dinga yin amfani da fararen hular domin samun kariya kafin a samu nasarar murkushe su daga karshe a Mosul, kuma gwamnatin Iraqin ta ayyana samun galaba kan mayakan na IS ne a ranar 10 ga watan Yuli.

Kubis ya jaddada yin kira da a tabbatar da kare fararen hula a lokacin tashin hankalin, kasancewa a halin yanzu Iraqin tana shirin kaddamar da munanan hare-hare domin kwato ragowar yankunan dake hannu mayakan IS a sassan kasar daban daban. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China