in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya taya Uhuru Kenyatta murnar sake lashe zaben shugaban kasar Kenya
2017-08-15 09:42:45 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon taya murna ga Uhuru Kenyatta, game da sake zabensa da aka yi a matsayin shugaban kasa.

Cikin sakon da ya aike a ranar Lahadi, Shugaba Xi Jinping ya ce ya na girmama ci gaban huldar dake tsakanin Sin da Kenya, kuma ya na fatan aiki da Shugaba Uhuru Kenyatta wajen zurfafa huldarsu domin moriyar kasashen biyu da al'ummominsu.

A ranar Juma'a da ta gabata da daddare ne aka ayyana Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Kenya, bayan ya samu kashi 54.27 na jimilar kuri'un da aka kada. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China