Rahotanni daga kasar Iraki na cewa, kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS ta ba da wata takaitacciyar sanarwa ta kafar yada labarunta a Tal Afar da ke yammacin birnin Mosul a yau Talata, cewa jagorarta Abu Bakr al-Baghdadi ya mutu, amma ba ta fayyace dalilin mutuwarsa ba, kana ta ce, nan ba da dadewa ba kungiyar za ta zabi sabon jagora. (Tasallah Yuan)