Cikin wata sanarwa, Guteress ya jinjinawa al'umma da Gwamnatin Iraqi saboda kwarin gwiwarsu da jajircewa da kuma juriya.
Sanarwar da aka fitar a jiya ta ruwaito cewa, MDD za ta ci gaba da goyon bayan Gwamnatin Iraqi kan ayyukan dake gabanta na yin dukkan abubuwan da suka kamata da ba da gudunmuwa don tabbatar da wadanda suka tsere daga muhallansu sun koma lami lafiya tare da dawo da tsarin mulki a yankunan da aka 'yanta da kare sake barkewar rikici da kuma daidaita duk wata doka da aka take.
A jiya Litinin ne Iraqi ta sanar da 'yanto birnin Mosul daga hannun kungiyar IS a hukumance, bayan an shafe watanni 9 ana gwabza kazamin fada don fatattakar mayakan daga tunkarsu ta karshe a Iraqi. (Fa'iza Mustapha)