in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar mai mulki ta Zimbabwe ta yi taro don nuna goyon baya ga shugaba Mugabe
2017-08-31 13:58:06 cri
Jiya Laraba, jam'iyyar mai mulkin kasar Zimbabwe ta ZANU-PF ta kira wani taro a birnin Harare, fadar mulkin kasa, domin nuna goyon baya ga shugaba Robert Gabriel Mugabe mai shekaru 93, game da burinsa na shiga babban zaben shugabancin kasar dake tafe a shekara mai zuwa.

An haifi Robert Gabriel Mugabe ne a ranar 21 ga watan Fabrairu na shekarar 1924, shi ne kuma babban shugaba da ya jagoranci 'yan rajin neman 'yancin kan al'ummomin kasashen Afirka.

Bayan aka sanar da samun 'yancin kan kasar Zimbabwe a shekarar 1980, ya dare matsayin firaministan kasar. Sa'an nan, ya zama shugaban kasar a shekarar 1987. Ya zuwa yanzu, yana ci gaba da shugabancin wannan kasa. Da yake wa'adin aikinsa zai cika a shekarar 2018 mai zuwa, hakan ya sa a watan Disamba na shekarar da ta wuce, jam'iyyar mai mulkin kasar Zimbabwe ta ZANU-PF ta sake tsayar da Mr. Mugabe a matsayin dan takarar ta a babban zaben dake tafe.

Tun daga farkon shekarar bana, ya zuwa yanzu, jam'iyyar ZANU-PF ta riga ta kira taruruka da dama domin neman goyon baya, haka kuma, yayin wani taron da aka yi a watan da ya gabata, shugaba Mugabe ya bayyana cewa, yana cikin koshin lafiya, kuma zai iya ci gaba da gudanar da ayyuka a matsayin shugaban kasar, amma, yana neman wanda zai gaje shi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China