Ana sa ran ganawar farko da shugaban kasar zai yi a Marondera, babban birnin lardin Mashonaland dake gabashin kasar, mai nisan kilomita 80 kudu da Harare, za ta hallara dubban matasa daga lardin da ma nesa, a daidai lokacin da jam'iyyar ke fama da barakar daka iya ba da damar kawar da Mugade mai shekaru 93 daga mulki.
Jaridar The Herald ta ruwaito sakataren matasa na jam'iyyar Kudzai Chipanga yana gargadin duk wasu masu wata manufa baya ga ganawar da shugaba Mugaben zai yi da matasan, da su nisanci taron.
Shugaba Mugabe zai yi tattaki zuwa dukkan lardunan mulkin kasar a lokacin ganawa da matasan, wadanda ake ganin a matsayin kashin bayan nasarar jam'iyyar a zaben dake tafe, biyo bayan takun sakan dake tsakanin Mugabe da wani bangare na tsoffin wadanda suka yi fafutukar kwatar 'yancin kasar. (Ibrahim Yaya)