in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a fara gwada na'urar samar da wutar lantarki mai aiki da karfin ruwa da kamfanin kasar Sin ya gina a kasar Zimbabwe
2017-06-05 11:29:00 cri
Ya zuwa yanzu an kammala kashi 85 cikin kashi dari na ayyukan kara yawan injunan samar da wutar lantarki masu aiki da karfin ruwa da aka sanya a cikin madatsar ruwa mafi girma da wani kamfanin kasar Sin ya gina a kudancin bankin kogin Kariba na kasar Zimbabwe. Inda a karshen wannan shekara ake sa ran gwada na'urar.

Mr. Yang Sheya, jami'in da ke kula da aikin ya bayyana a jiya Lahadi, cewa za a gama aikin sanya injin samar da wutar lantarki na daban a farkon shekara mai zuwa. Sakamakon haka, injunan biyu za su iya samar da wutar lantarki ga cibiyoyin samar da wutar lantarkin kasar Zimbabwe, ta yadda za a iya magance matsalar karancin wutar lantarki da kasar Zimbabwe take fuskanta.

Mr. Huang Ping, jakadan kasar Sin dake kasar Zimbabwe ya bayyana cewa, wannan aiki zai samar wa kasar Zimbabwe karin wutar lantarki, ta yadda al'ummar kasar za ta samu moriya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China