in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe: mutane 8 sun rasa rayukansu sakamakon ruftawar mahakar zinariya
2017-05-30 12:24:24 cri

Rundunar 'yan sandan kasar Zimbabwe ta bayyana jiya Litinin cewa, mutane 8 sun rasa rayukansu sakamakon ruftawar mahakar zinariya a kwanan baya.

Kamfanin dillancin labarun kasar Zimbabwe ya ruwaito kakakin rundunar 'yan sandan kasar na cewa, an tafiyar da wannan mahakar zinariya ce ba bisa doka ba, kuma dukkan mutanen 8 da suka rasa rayukansu, masu hakar zinariya ne wadanda ba su da lasisi. Yanzu 'yan sandan suna bin bahasin musabbabin ruftawar wannan mahakar zinariya, sa'an nan kuma sun kara karfinsu na yaki da hakar ma'adinai ba bisa doka ba.

Hakar zinariya ba bisa doka ba ta zama ruwan dare a kasar ta Zimbabwe. Mutane da dama na hakar zinariya ba bisa doka ba kuma ba tare da daukar matakan tabbatar da tsaron lafiyarsu ba duk da nufin samun kudin kashewa. Daga lokaci zuwa lokaci ruftawar mahakar ma'adinai a kasar kan yi sanadiyar mutuwar mutane tare da jikkata wasu a kasar. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China