in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afirka na fatan kara yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin makamashi da kayayyakin more rayuwar al'umma
2017-06-05 14:32:16 cri
A kwanan baya ne, jakadun wasu kasashen Afirka dake kasar Zimbabwe suka kai ziyara madatsar ruwar dake kudancin bankin kogin Kariba, inda wani kamfanin kasar Sin yake aikin kara injunan samar da wutar lantarki masu aiki da karfin ruwa.

A yayin da suke madatsar ruwan, jakadun sun yaba da kamfanin na kasar Sin ya kammala aikin cikin sauri da kuma inganci, inda suka yi fatan kasashensu za su kara yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin samar da makamashi da kayayyakin more rayuwar al'umma.

Jakada Mwana Nanga Mawanmpanga na kasar Kongo Kinshasha dake kasar Zimbabwe ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasance abin koyi ga kasashen Afirka wajen neman ci gaba. Kasar Sin na amfani da fasahohinta na zamani wajen samar da kayayyakin more rayuwar al'umma ga kasashen Afirka, domin taimakawa kasashen Afirka wajen neman ci gaba cikin sauri. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China