Da yake jawabi jiya Jumma'a, yayin wani taro kan huldar kasuwanci tsakanin Afrika ta kudu da Zimbabwe, wanda ya gudana a Johannesburg, Emmerson Mnangagwa ya ce al'ummar Afrika na da matukar muhimmanci a yaki da cin hanci, yana mai kira gare su su hada hannu da gwamnatoci wajen yakarsa.
Ya ce batun cin hanci babbar matsala ce a Afrika, wadda ta damu gwamnati ba kadai a Zimbabwe ba, har ma a nahiyar baki daya.
A bara ne wata kungiyar al'umma ta kasa da kasa mai suna Transparency International ta ruwaito cewa, Zimbabwe na asarar a kalla dalar Amurka biliyan 1 a kowace shekara saboda cin hanci, inda ta bayyana jami'an 'yan sanda da na gwamnati a matsayin manyan masu aikata laifin.
Makasudin taron na yini biyu shi ne, lalubo damarmakin cinikayya da zuba jari da ba a amfani da su, a tsakanin kasashen biyu. (Fa'iza Mustapha)