Mr. Wu ya bayyana haka ne a jiya Juma'a, yayin wani taron kan kasar Afghanistan da kwamitin sulhu na MDD ya kira.
Bugu da kari, ya ce, ya kamata gamayyar kasa da kasa su gaggauta cimma alkawarin da suka dauka na bada taimako ga kasar Afghanistan, da kuma ba ta goyon baya wajen raya tattalin arzikinta.
Ya kuma kara da cewa, kasar Afghanistan za ta ba da gudumawa matuka ga bunkasar tattalin arzikin yankin, sakamakon albarkatun da kasar take da su.
Haka kuma, babban taron MDD da kwamitin sulhun, sun amince cewa shirin zirin tattalin arziki ta hanyar siliki zai taimakawa kasar Afghanistan wajen raya tattalin arzikinta, da kuma habaka hadin gwiwa a tsakaninta da sassa daban-daban dake yankin.
Ana sa ran bangarorin da abin ya shafa za su inganta shirin zirin tattalin arziki ta hanyar siliki cikin hadin gwiwa, ta yadda za a iya karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kuma mu'amala tsakanin sassa daban-daban a yankin. (Maryam)