Gwamnan jihar Borno dake arewa maso gabashin tarayyar Najeriya Kashim Shettima, ya ce mayakan kungiyar Boko Haram, sun hallaka masunta a kalla 31, yayin wasu tagwayen hare-hare da suka kaddamar a garin Baga dake jihar Borno.
Gwamnan ya ce, mayakan kungiyar sun kai hare-hare a garin na Baga ne tsakanin ranekun Asabar da Lahadi, kuma bisa rahotanni da gwamnatinsa ke samu, har yanzu mayakan kungiyar na farwa fararen hula a sassan arewa maso gabashi, da yankunan tafkin Chadi mai makwaftaka.(Saminu)