Jami'in ya bayyanawa manema labarai a Abuja babban birnin kasar cewa, gwamnatin Najeriyar tana yin kira ga magoya bayan kungiyar ta Boko Haram da su amince su mika wuya kuma su rungumi shirin zaman lafiya.
A cewar Olonisakin, babban abin da gwamnatin ta fi mayar da hankali kansa shine, sauya tunani, gyaran hali, da kuma sake maidowa tsoffin mayakan na Boko Haram tunaninsu domin su samu damar komawa hayyacinsu don cigaba da gudanar da rayuwar cikin alumma.
Yace a halin yanzu akwai tsaoffin mayakan 'yan tada kayar bayan su 96 a wani sansani dake jahar Gombe arewa maso gabashin kasar, kana akwai wasu mata da kananan yara su 565, wadanda zasu halarci shirin sauya tunanin na tsawon makonni 12.(Ahmad Fagam)