in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram ta kashe mutane 6 yayin wani hari a arewa maso gabashin Najeriya
2017-08-03 09:34:05 cri
Da sanyin safiyar ranar Laraba kungiyar Boko Haram ta hallaka mutane 6 a wani kauye dake arewa maso gabashin Najeriya.

Ahmad Sajoh, shi ne kwamishinan yada labarai na jihar Adamawa dake arewa maso gabashin kasar ya shedawa kamfanin dillanci labarai na Xinhua cewa, a kokarin dakile harin, wasu maharba a kauyen Midlu dake karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa sun hallaka daya daga cikin mayakan na Boko Haram.

Sajoh, ya ce wani yunkuri na hadin gwiwa tsakanin sojoji da maharba ya sa an yi nasarar fatattakar maharan daga kauyen.

Wasu jami'an yankin sun bayyana cewa, harin ya yi sanadiyyar mafi yawa daga cikin mazauna kauyen sun tsere, yankin ya kunshi wajen nan na Sukur mai dadadden tarihi wanda hukumar raya ilmin da al'adu ta MDD UNESCO, ta ware a matsayin wajen tarihi, wanda Boko Haram suka lalata shekaru 3 da suka gabata. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China