Shugaban kungiyar malaman jami'o'i reshen jami'ar Maiduguri(ASUU)Dani Mamman ya bayyana cewa, galibin malaman da suka ajiye aikin nasu farfesoshi ne, da suka kware a fannonin bincike da koyarwa a jami'ar.
Mamman ya kuma shaidawa manema labarai a ranar Asabar din da ta gabata cewa, daya daga cikin dalilan da suka harzuka malaman barin jami'ar shi ne, harin baya-bayan da Boko Haram ta kaiwa abokan aikinsu, inda aka kashe malaman jami'ar biyar kana har yanzu ba a ji duriyar wasu uku da kungiyar ta yi garkuwa da su ba.
A makonni biyu da suka gabata ne dai mayakan Boko Haram suka yiwa malaman jami'ar kwanton bauna a yayin da suke aikin binciken mai tare da ma'aikatan hukumar samar da mai ta Najeriya a yankin tafkin Chadi.(Ibrahim)