in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mayakan Boko Haram 100 ne dakarun sojin kasar Kamaru suka hallaka
2015-12-03 20:53:09 cri
Kakakin rundunar sojojin kasar Kamaru Kanar Didier Badjeck, ya shaidawa wani taron manema labarai cewa, sojojin kasar sa sun hallaka mayakan kungiyar Boko Haram sama da 100, ciki hadda wani kusa a kungiyar mai suna Al Hadji Gana, kana sun kubutar da mutane 900 da kungiyar ke garkuwa da su, a simamen da suka gudanar kan sansanonin kungiyar, tsakanin ranekun 26 zuwa 28 ga watan Nuwambar da ya shude.

Kanar Badjeck ya kara da cewa sojojin na Kamaru, sun gudanar da simamen ne a wasu yankuna dake yammacin kasar mai iyaka da Najeriya.

Sassan da sojojin suka yiwa dirar mikiya sun hada da kauyen Mayo-Sava, dake yankin arewa mai nisa, inda suka fatattaki mayakan kungiyar, tare da kwace makamai masu yawa, da kuma tutocin kungiyar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China