Yau Alhamis ne Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a nan Beijing cewa, girke na'urorin kakkabo makamai masu linzami samfurin THAAD da kasar Amurka take yi a kasar Koriya ta Kudu, yana barazana ga harkokin tsaron kasar Sin, tare da lalata daidaito a yankin, kuma lamarin ba zai taimaka a kokarin da ake na kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya da kuma wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin ba. kasar Sin ba ta goyi bayan wannan mataki
Rahotanni na cewa, Amurka ta kai na'urorin kakkabo makamai masu linzami gami da nau'rorin harba makamai masu linzama guda 4 zuwa Koriya ta Kudu a asirce. (Tasallah Yuan)