Mr. Geng Shuang wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai, ya ce batun yanayin da ake ciki a zirin Koriya na da sarkakiya, don haka Sin ke fatan dukkanin sassan da batun ya shafa za su kai zuciya nesa, domin kaiwa ga magance dukkanin matsaloli, tare da tabbatar da tsarin zaman lafiya da lumana a zirin.
Manyan jami'an tsaron kasar Koriya ta kudu dai sun fidda wata sanarwa a Talatar nan, suna masu korafin cewa koriya ta arewa ta harba makami mai linzami a gabar ruwan gabashin yankin ta da ke kusa da Banghyeon, wanda ke arewa da birnin Pyongan, da misalin karfe 10 saura minti 20 na safiya bisa agogon yankin.
Daga bisani ita ma koriya ta arewan ta tabbatar da gwajin makamin wanda ke cin dogon zango, tana mai bayyana shi da wani gagarumin ci gaba a shirin ta na bunkasa makamai masu linzami.(Saminu Alhassan)