A wani labarin kuma, shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya ce gwamnatinsa za ta kara daura damar yaki da kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram, wadda a halin yanzu take kaddamar da sabbin hare-hare a wasu wuraren da babu jami'an tsaro.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne cikin jawabinsa na farko da ya gabatar wa 'yan kasar ta kafofin watsa labarai, tun bayan dawowarsa daga hutun jinyar da ya kwashe kwanaki 104 a birnin Landan na kasar Burtaniya.
Ya kuma bukaci hukumomin tsaro, da kada nasarorin da suka samu cikin watanni 18 din da suka gabata su rage musu kaimi a yakin da suke yi da mayakn Boko Haram.
Buhari ya ce, wajibi ne mu yaki, 'yan ta'adda da bata gari, har sai mun ga bayan su kwata-kwata, ta yadda za mu zauna cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. (Ibrahim)