Shugaba Buhari, wanda ya samu tarbar mataimakinsa, Yemi Osinbajo a hukumance, wanda shi ne ya jagoranci kasar na wucin gadi a lokacin da shugaban ya tafi hutun.
Manyan jami'an gwamnatin kasar da dama ne suka tarbi shugaban a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe na kasa da kasa dake Abuja.
Shugaban ya tafi hutun ne a ranar 7 ga watan Mayu, kuma gabanin tafiyar tasa ya damka ragamar shugabancin kasar a hannun mataimakinsa Osinbajo.
Shugaban na Najeriya mai shekaru 74, ya tafi hutun ne watanni biyu bayan dawowarsa daga makamancin hutun, gabanin tafiyar tasa ya karbi 'yan matan Chibok da Boko Haram ta sake su.
A lokacin da yake hutun jinyar a Landan, shugaba Buhari, ya samu ziyartar manyan kusoshin Najeriyar, inda mataimakin shugaban kasar ne ya fara ziyartarsa, inda kuma ya bayyana wa al'ummar Najeriyar game da irin halin da shugaban kasar ke ciki na samun sauki daga jinyar da yake fama da ita.
Buhari, wanda tsohon janar din soja ne, ya sha bayyanawa wadanda suke ziyartar tasa cewa yana matukar samun sauki, amma yana jiran umarnin likitoci ne, wanda ya ce a baya shi ne yake ba da umarni, amma a yanzu shi ne ake baiwa umarnin. (Ahmad Fagam)