in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya jaddada bukatar hada kan kasa
2017-08-21 20:21:52 cri

A yau Litinin ne, shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi wa al'ummar kasar jawabinsa na farko tun bayan da ya dawo daga dogon hutun jinyar da yake a birnin Landan a ranar Asabar din da ta gabata, yana mai cewa, batun hadin kan kasa, batu ne da aka riga aka cimma matsaya a kai kuma ba za a sake waiwayarsa ba.

Shugaba Buhari ya kuma yi Allah wadai da kalaman baya-bayan da wasu ke yi, musamman a shafukan sada zumunta game da makomar hadin kan kasar.

Don haka ya yi kira ga 'yan Najeriya, ba tare bambamcin kabila ko addini ba, da su guji duk wasu abubuwan da za su raba kan kasar, maimakon haka su mayar da hankali wajen tunkarar kalubalen tattalin arziki, tsaro, siyasa da kasar take fuskanta, su kuma hada kai tare da tabbatar da zaman lafiya da sauransu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China