Yemi Osinbajo ya bayyana haka ne a jiya, lokacin da yake jawabi ga taron majalisar tsaro, wanda majalisar kula da tattalin arizikin kasar ta shirya a Abuja.
A cewarsa, tsorata mutane da kalaman baatanci aikin ta'addanci ne kuma gwamnati ta kuduri niyyar daukar batun da gaske.
Mukaddashin shugaban kasar ya yi kira ga shugabannin addinai da na kasuwanci da na siyasa su yi tir da kalaman baatanci da kakkausar murya, musamman idan irin kalaman suka fito daga mabiya addininsu ko kabila.
Ya ce yin shiru game da irin wadanan furuci tamkar amincewa da su ne.
Har ila yau, ya kuma jadadda cewa, jigon manufar gwamnatin ita ce, tsare rayuka da dukiyar al'umma, yana mai cewa gwamnatin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen cimma wannan manufa.
Yemi Osinbajo ya ce ya lura da cewa, idan ana son magance matsalar rashin tsaro, to akwai bukatar dukkan matakan gwamnati su yaki fatara. (Fa'iza Mustapha)