Ministan kimiya da fasaha na Najeriya Ogbonnaya Onu wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja, babban birnin kasar, ya ce kundin da aka tsara zai taimakawa bangaren kimiyar kasar wajen raya tattalin arziki da jin dadin rayuwar al'ummar Najeriya.
Ministan ya ce sabon tsarin zai kuma baiwa Najeriya damar samar da abubuwan da take bukata kana ta fitar da ragowar zuwa sassan duniya, a hannu guda kuma zai baiwa Najeriyar damar adana kudaden asusunta na ajiyar ketare, baya ga karfafa harkokin cinikayyarta na ketare duk da nufin taimakawa tattalin arzikin kasar.
Najeriya kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka, ta bullo da wannan shiri ne da nufin kartata hankalinta zuwa ga bangaren kimiya, da fasaha da kirkire-kirkire a matsayin kashin bayan shirinta na raya kasa. (Ibrahim Yaya)