in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya tana kokarin rage kudaden hako mai a kasar
2017-08-18 09:32:30 cri
Mahukuntan Najeriya sun bayyana kudurinsu na rage kudaden da ake kashewa wajen aikin hako mai daga dala 32 kan kowace ganga zuwa dala 15 kan kowace ganganr mai, ta yadda hakan zai rage kudaden da masu zuba jari daga ketare ke kashewa.

Ministan albarkatun mai na Najeriya Ibe Kachikuwu wanda ya bayyana hakan a birnin Legas, cibiyar kasuwancin kasar, ya ce kudaden da ake kashewa suna kara harkar zuba jari kai tsaya ta kara tsada.

Ministan ya ce an tsara dokar tafiyar da masana'antar man kasar (PIGB) da nufin inganta bangaren samar da man kasar ta yadda hakan zai iya janyo masu sha'awar zuba jari.

Kachikwu ya ce batutuwan tsaro da karancin kudi da matatun man kasar ke fuskanta, sun taimaka wajen jinkirta fara aikin matatun man kasar, ko da an bayar da lasisi. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China