in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hare-haren kunar bakin waken sun halaka mutane 19 a yankin arewa maso gabashin Najeriya
2017-08-16 18:49:19 cri
Kwamishinan 'yan sanda na jihar Borno Damian Chukwu ya tabbatar da cewa, mutane 19 ciki har da 'yan kunar bakin wake uku ne suka gamu da ajalinsu kana wasu 82 kuma suka jikkata, sanadiyar wasu tagwayen hare-hare da aka kaddamar a garin Konduga dake yankin arewa maso gabashin kasar.

A cewarsa,wasu mata 'yan kunar bakin wake guda biyu ne da kuma wata mace ta daban suka kaddamar da hare-haren a wata kasuwa mai cike da mutane a garin na Konduga.

Sai dai kuma rahotanni na cewa, a kalla mutane 27 ne suka mutu sanadiyar hare-haren.

Ana dai zargin kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram da kai wadannan hare-hare.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China