An gudanar da shawarwarin harkokin waje da kiyaye tsaro a tsakanin Sin da Amurka na zagaye na farko a kasar Amurka
A jiya ranar 21 ga wata, mamban majalisar gudanarwa na kasar Sin Yang Jiechi, da sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, da ministan tsaron kasar Amurka Jim Mattis, sun shugabanci shawarwarin harkokin waje da kiyaye tsaro a tsakanin Sin da Amurka na zagaye na farko tare a birnin Washington dake kasar Amurka.
A gun shawarwarin, bangarorin biyu sun bayyana cewa, za a ci gaba da aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito, da fadada fannonin hadin gwiwar samun moriyar juna, da warware matsaloli bisa tushen girmama juna, da sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata a dogon lokaci. (Zainab)