in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Iraqi ya nemi rundunar Sojin kasar ta ba da tabbacin tsaro a Birnin Mosul
2017-07-10 09:44:39 cri

Firaministan Iraqi Haidar Al-Abadi, ya bukaci rundunar sojin kasar ta kakkabe ragowar mayakan IS tare da tabbatar da tsaro a birnin Mosul.

Wata sanarwar da ofishin Firaministan ya fitar a jiya ta ce, Haidar Al Abadi ya bada umarnin ne yayin taron da ya yi da kwamandojin soji, jim kadan bayan isarsa birnin na Mosul, inda ya kuma taya su murnar kwace iko da garin daga hannun kungiyar IS.

Firaministan ya jadadda cewa, sojoji za su fattataki ragowar mayakan IS dake Mosul, sannan su kwance nakiyoyi da aka binne da sauran ababen fashewa tare da tsaron fararen hula da wadanda suka rasa matsugunansu domin tabbatar da tsaro a baki dayan birnin.

Haidar Abadi ya ayyana samun nasarar a kan kungiyar IS, bayan an shafe kwanaki 266 ana kwabza kazamin fadan da ya kai ga 'yantar da birnin da kuma kawo karshen iko da shi da kungiyar ta shafe shekaru 3 ta na yi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China