Ministan tsaron Iran Hossein Dehqan, ya bayyana a jiya cewa, yana da yakinin samun nasara da fatattakar 'yan ta'addan abu ne mai yiwuwa, idan gwamnatoci suka jajirce wajen yaki da ayyukan ta'addanci.
Har ila yau, sakataren majalisar koli kan harkokin tsaro na Iran Ali Shamkhani, ya alakanta 'yanto birnin Mosul da kyakkyawan jagorancin shugaban addini da hangen nesa irin na Gwamnatin Iraqi da kuma kwarin gwiwar sojojin kasar da dakaru 'yan sa kai.
Ali Shamkhani ya bayyana fatan cewa, nasarar da aka samu kan kungiyar IS, zai zama mafarin farfado da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da ci gaban kasar Iraqi. (Fa'iza Mustapha)