in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Iraqi ya ayyana 'yanto birnin Mosul daga mayakan IS
2017-07-11 10:47:18 cri
Firaministan kasar Iraqi Haider al-Abadi, ya ayyana 'yanto birnin Mosul daga mayakan IS. Mr. Al-Abadi wanda ya shelanta hakan a jiya Litinin, ya ce daga wannan rana, daukacin yankunan birnin na Mosul sun koma karkashin ikon gwamnatin Iraqi a hukunce.

Cikin wani jawabi da ya gabata, Al-Abadi ya ce "Ina shaidawa duniya cewa yaki ya kare, mun karya lagon kungiyar 'yan ta'adda ta IS, kamar yadda suka ayyana karbe ikon wannan birni shekaru 3 da suka gabata."

A ranar Lahadi ne dai Mr. Abadi, wanda kuma shi ne babban kwamandan rundunar sojojin kasar ta Iraqi, ya ziyarci birnin na Mosul inda ya gana da manyan jami'an rundunar sojin kasar, kafin kuma ya zagaya sassan gabashin birnin inda daruruwan jama'a suka yi masa maraba.

Bayan hakan ne kuma Mr. Abadi ya fidda wata sanarwa dake cewa, sojojin kasar Iraqi sun samu cikakkiyar nasarar da suke fata, kuma ba abun da ya ragewa 'yan ta'addan sai dan abun da ba a rasa ba.

A ranar 17 ga watan Oktobar bara ne Firaministan na Iraqi, ya shelanta kaddamar da hare-haren kwato birnin na Mosul, wanda shi ne birni na biyu mafi girma a dukkanin fadin kasar.

Tun daga wannan lokaci ne kuma jami'an tsaro a Iraqi ke ta dannawa sassan birnin tare da yi masa kawanya, inda suka rika dauki ba dadi da mayakan na IS, ya zuwa wannan lokaci da suka fatattake su baki daya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China