in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar editocin Nijeriya sun ziyarci sabon yankin Binhai na birnin Tianjin
2017-07-28 13:55:31 cri

Tawagar editocin tarayyar Nijeriya, sun kai ziyara sabon yankin Binhai dake birnin Tianjin na kasar Sin a jiya Alhamis, inda suka ziyarci tashar samar da wutar lantarki da hasken rana ta Xinyi da kuma reshen kamfanin tsimin makamashi da kiyaye muhalli na kasar Sin dake birnin na Tianjin.

A yayin ziyarar, an yi musu takaitaccen bayani kan yanayin da kamfanonin ke ciki da kuma fasahohin zamanin da suke amfani da su.

Yan jaridar sun yi fatan cewa, za a karfafa hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasar Nijeriya a wadannan fannoni. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China