Cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya Laraba, Mr. Kachikwu ya ce tsarin dake kunshe cikin wani kundi mai shafuka 100, na da nufin kawar da duk wani shinge dake dakile zuba jari ga masu sha'awa, ya kuma tabo duk wasu muhimman sassa na hada hadar albarkatun mai.
Bugu da kari, tsarin ya fayyace matsayin hukumomin gwamnati da sassa masu zaman kan su, game da rawar da kowa ke da ikon takawa a fannin hada hadar mai.
Kaza lika Kachikwu ya jaddada kudurin ma'aikatar sa, game da inganta ayyukan tace albarkatun mai a cikin gida, ta hanyar kyautata ayyukan matatun mai, da kawo karshen shigar da man daga ketare, musamman bisa la'akari da yadda farashin danyen man ke cikin wani yanayi na rashin tabbas.