in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar binciken Gambiya ta fara nazari kan ta'ammalin da tsohon shugaban kasar ya gudanar
2017-08-11 10:20:36 cri

Hukumar binciken da gwamnatin kasar Gambiya ta kafa domin duba yadda tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya tafiyar da harkokin kudaden baitulmalin kasar ta fara sauraron ra'ayoyin jama'a karo na farko a ranar Alhamis, inda aka samu zarge-zarge masu karfi game da yadda aka tafiyar da harkokin kudaden kasar, kamar yadda wasu manajojin hukumomin kudaden kasar 4 suka ba da shaida.

Shugaban hukumar binciken Surahatta Semega Janneh ya ce, babban dalilin da ya sanya aka gudanar da taron jin ra'ayoyin jama'ar shi ne, domin tabbatar da cewa, an gudanar da aikin a bayyane karara.

Kamar yadda Surahatta Semega Janneh ya sanar, an kafa hukumar ne domin bincikar yadda tsahon shugabann kasar da mataimakansa suka tafiyar da sha'anin kudaden da dukiyoyinsa a lokacin da yake jan ragamar shugabancin kasar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China