in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin musamman na shugaban kasar Sin zai halarci bikin rantsar da shugaban Gambiya
2017-02-16 20:08:17 cri

Mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin mista Ma Peihua, wanda ke matsayin wakilin musamman na shugaba Xi Jinping na kasar, zai halarci bikin rantsar da shugaban kasar Gambiya mista Adama Barrow, da kuma bikin murnar ranar samun 'yancin kan Gambiya, wanda za a gudanar a ranar 18 ga wata a birnin Banjul, hedkwatar Gambiya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya fadi hakan a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing yau Alhamis. Ya kuma kara da cewa, kasar Sin ta yaba wa sabuwar gwamnatin Gambiya karkashin shugabancin Mr. Barrow, bisa amincewar ta da manufar "kasar Sin daya tak a duniya", tana kuma fatan yin kokari tare da Gambiya wajen zurfafa hadin gwiwar abokantaka a tsakanin kasashen 2 daga dukkan fannoni, da kuma kawo wa jama'arsu duka alheri. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China