in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta jinjinawa ECOWAS game da rawar data taka wajen warware dambarwar siyasar Gambiya
2017-02-01 12:44:34 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yabawa namijin kokarin da kungiyar raya cigaban tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta yi, wajen bin hanyoyin lumana don kafa sabuwar gwamnatin kasar Gambiya.

Da yake jawabi a taron kungiyar tarayyar Afrika AU karo na 28 a Litinin din data gabata, mista Guterres, ya ce hadin kan kungiyar ECOWAS da kuma hakurin da al'ummar kasar Gambiya suka nuna wajen warware rikita rikitar siyasar kasar abin a yaba ne.

Tsohon shugaban kasar Gambiyan Yahya Jammeh ya fita daga kasar ta Gambia cikin kwanciyar hankali, bayan shiga tsakanin da kungiyar ta ECOWAS ta yi, tun bayan da ya ki amincewa ya mika mulki ga shugaban kasar Adama Barrow wanda ya kada shi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Disambar 2016.

Nkosazana Dlamini-Zuma, shugabar kungiyar AU mai barin gado, ita ce ta jagoranci tawagar shugabanni don karrama kungiyar ta ECOWAS a kokarin data nuna na tabbatar da mika mulkin cikin kwanciyar hankali a Gambia.

Shugabar Liberiya Johnson Sirleaf ce ta karbi lambar yabon a madadin kungiyar ECOWAS.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China