in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin wajen Sin da Gambiya sun yi shawarwari a tsakaninsu
2017-08-01 21:07:22 cri

A yau Talata 1 ga watan Agusta ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Gambiya Ousainou Darboe.

A yayin shawarwarin da suka gudanar a nan Beijing, Wang Yi ya ce, kasar Sin ta yaba wa gwamnatin Gambiya bisa goyon bayan ta ga manufar "kasar Sin daya tak a duniya". da kuma himmantuwa wajen kyautata zumuncin da ke tsakaninta da Sin. Kaza lika kasar Sin tana fatan zurfafa aminci da juna ta fuskar siyasa a tsakaninta da Gambiya, don haka ya dace sassan biyu su yi amfani da fifikon da suke da shi, wajen inganta hadin gwiwar da ke tsakaninsu a fannonin samar da ababen more rayuwar jama'a, da aikin gona, da sashen harkokin bude ido da dai sauransu. Sa'an nan Sin na fatan inganta mu'amalar a tsakanin jama'ar ta da bangaren Gambiya, da kara taimakawa juna a al'amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya, a kokarin daga matsayin huldar da ke tsakanin kasashen 2 zuwa wani sabon mataki.

A nasa bangaren kuma, mista Darboe ya ce, gwamnatin Gambiya da jama'ar kasar na gode wa kasar Sin bisa goyon baya da taimako da take bayarwa, wajen farfado da kasar Gambiya. Kana kuma Gambiya za ta ci gaba da bin manufar "kasar Sin daya tak a duniya", tana kuma sa ran inganta hadin gwiwa a tsakaninta da Sin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China