in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gambiya za ta yiwa dokar aikin jarida kwaskwarima
2017-07-06 11:14:29 cri
Gwamnatin kasar Gambiya ta sanar a ranar Laraba cewa, an fara yin garambawul ga dokokin da suka shafi aikin jarida a kasar.

Demba Ali Jawo, shi ne ministan watsa labarai da samar da kayayyakin sadarwa na kasar ya ce, kafafen yada labaran kasar suna bukatar a samar musu dokokin da za su ba su damar gudanar da ayyukansu ba tare da yin katsa landan ba.

Ya ce akwai bukatar a yi wa dokokin da aka gada daga tsohuwar gwamnatin kasar gyaran fuska, wadanda suka ba da damar kamawa da kuma garkame 'yan jaridun kasar ta Gambiya da dama a gidajen yari.

Jawo ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, a halin yanzu akwai wani kwamiti da suka kafa tare da hadin gwiwar kungiyar 'yan jaridun kasar Gambiyan. Ya ce wannan kwamitin shi zai tsara jadawalin yadda za'a gudanar da gyaran fuskar ga dokokin aikin jarida a kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China