in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Ghana za ta yi amfani da asusun ajiya daya tilo don inganta sha'anin kudi
2017-08-11 09:36:17 cri

A kokarinta na bunkasa fannin harkokin kudi da daukar matakai masu inganci, gwamnatin kasar Ghana ta kaddamar da shirin yin amfani da asusun ajiya na TSA kwaya daya tak a kasar.

Wannan mataki zai taimaka wa gwamnatin kasar ta samu damar gudanar da tsarin ajiya na ma'aikatu da hukumomin gwamnati na kasar baki daya.

Ministan kudin kasar Kenneth Ofori-Atta, ya bayyana yin amfani da tsarin na TSA da cewa, ya zama tilas domin hakan zai baiwa gwamnatin kasar damar tsara harkokin kudinta, kuma zai hana yin ajiyar kudaden riba da gwamnatin ke samu, wanda galibi bankunan kasar ke amfani da su wajen sayan takardun lamuni da na yarjejeniyar hada-hadar kudade.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China