Peter Atimka Anaadumba, shugaban shirin hadin gwiwar Sin da kasashe maso tasowa ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ofishin FAO mai kula da al'amurran shiyyar Afrika, ya ce an yi amana cewa kasar Sin ta shafe shekaru masu yawa tana yin hadn gwiwa da kasashen kudu da hamadar saharar Afrika wajen sauya fasalin aikin noma.
Peter ya bayyana hakan ne a lokacin taron bita na wuni biyu don yin musayar ilmi game da yadda za'a bunkasa aikin noman shinkafa a Elmina, wanda ke da nisan kilomita 158 daga yammacin Accra, babban birnin kasar Ghana.
Ya ce kasar Sin babbar jigo ce idan ana maganar hadin gwiwa da kasashen Afrika. Babbar abokiyar huldar shirin samar da abinci da inganta noma na FAO ne. Idan aka duba Afrika, kasar Sin ta bayar da kudade ga shirin FAO a shekarar 2009 kimanin dala miliyan 30 kuma a kwanan nan ta bayar da dala miliyan 50, baki yada adadin ya kai dala miliyan 80, kuma wadannan kudaden da ta samar za'a yi amfani da su wajen ba da tallafi ga kasashen hamadar saharar Afrika wajen aikin samar da kwararru.
Ya yabawa kasar Sin game da wannan tallafin wanda a cewarsa yana samar da alfanu mai yawa wajen habaka aikin gona a kasashen Afrika. (Ahmad Fagam)