An tura runduna mai mambobi 400 da aka kafa a jiya zuwa yankunan Ashanti da gabashi da yammacin kasar, inda ayyukan suka fi kamari.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya jadadda kudurin gwamnatinsa na kawo karshen hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.
Kaddamar da rundunar mai suna "Operation Vanguard" ya zo ne kasa da wata guda bayan mutane 24 sun fada tare da mutuwa a cikin wani ramin hakar ma'adinai a yankunan Ashanti da yammacin kasar.
Bayan bikin kaddammar da rundunar, Ministan muhalli da kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire na kasar Kwabena Frimpong Boateng, ya bukaci dakarun sun gudanar da ayyukansu bisa biyayya ga doka tare da kauracewa take hakkokin mazauna yankunan.
Ana sa ran rundunar za ta kasance a yankunan har zuwa lokacin da za a farfado da yankunan da koguna da suka lalace da kuma cimma shirin farfado da dazuka. (Fa'iza Mustapha)