Mr. Maafo wanda ya bayyana hakan, yayin wani dandalin tattaunawa game da tattalin arzikin kasar da ya gudana jiya Litinin, ya ce dokar za ta kunshi hukunci ga jami'an gwamnati da suka sabawa tanadinta.
Ministan ya kara da cewa, dokar na da nufin ceto kasar Ghana daga matsaloli masu alaka da bunkasar tattalin arziki. (Saminu Hassan)