A jawabinsa na farko yayin bitar kasafin kudin kasar na rabin shekara a gaban majalisar dokokin kasar, ministan kudin kasar Ken Ofori-Attah, ya bayyana cewa, an sake rage kudaden da za a kashe ta yadda zai yi kasa da yawan kudaden haraji da aka yi hasashen tarawa, ta yadda zai yi daidai da abin da aka kasafta a tsarin kasafin kudin kasar.
Ministan ya ce an kuma sake rage kudaden haraji da tallafi da aka yi hasashen samu ya zuwa kaso 0.9 cikin 100 na alkaluman GDPn kasar, wato daga kudin kasar Cedi biliyan 44.5 kwatankwacin dala biliyan 10.11 zuwa Cedi biliyan 43.1. Bugu da kari, an rage jimmalar kudaden da aka yi hasashe kashewa da kaso 1.1 cikin 100 na GDPn kasar wato daga Cedi biliyan 58.1 zuwa Cedi biliyan 55.9.
Ya ce, bayan gudanar da wadannan gyare-gyare, ana fatan gibin kasafin kudin kasar zai ragu daga Cedi biliyan 13.2 wato kaso 6.5 cikin 100 na alkaluman GDPn kasar, zuwa Cedi biliyan 12.8 cikin 100, kaso 6.3 cikin 100 ke nan na alkaluman GDPn kasar ta Ghana.
Ko da yake ba a canja hasashen da aka yi game da samun karuwar kaso 6.3 cikin na GDP a wannan shekara ta 2017 ba, amma ministan ya sanar da rage hasashen ci gaban GDPn daga Cedi biliyan 203.41 zuwa Cedi biliyan 202.01. (Ibrahim Yaya)