Da yake ganawa da manema labarai a jiya Jumma'a, diraktan zartaswa na sashen kula da namun dawa na hukumar lura da gandun daji ta kasar Nana Kofia Adu-Nsiah, ya shaidawa manema labarai cewa, hukumomi ba za su lamuncewa duk wani dake kokarin amfani da kasar a matsayin wajen yada zagon yayin da yake safarar namun daji ba.
Nana Kofia Adu Nsiah, ya bayyana haka ne lokacin da yake mai da martani ga labaran da ake yadawa a kafofin watsa labarai na kasashen ketare game da kwace kilogram 393.50 na kwanson dabbar pangolin a kasar Malaysia cikin watan Yunin bana, wanda ake zargin ya fito daga Ghana.
Ya kara da cewa, a bayyane yake masu safarar namun daji na amfani da Ghana a matsayin wajen yada zango yayin da suke gudanar da mummunan aikinsu.
A don haka, suke son aikewa da sako da kakkausar murya gare su cewa, ba su da muhalli a Ghana, yana mai cewa za su zakulo su.
Har ila yau, ya jadadda cewa za a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin jami'an hana fasa kauri da na 'yan sanda da jami'an filayen jirgin sama da jami'an sirri kaya domin kawo karshen al'amarin. (Fa'iza Mustapha)