in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin sarrafa iskar gas da kasar Sin ta gina zai sauya fasalin tattalin arzikin kasar Ghana
2017-08-10 10:32:43 cri
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya bayyana a ranar Laraba cewa, kamfanin sarrafa iskar gas da kasar Sin ta gina a kasarsa a yankin Atuabo, mai tazarar kilomita 218 daga yammacin Accra, babban birnin kasar, wani muhimmin kayan more rayuwa ne wanda zai taimaka wajen sauya fasalin tattalinn arzikin kasar.

Da yake jawabi a lokacin da ya ziyarci aikin wanda kamfanin Sinopec na kasar Sin ya gudanar, wanda kuma shi ne kamfanin tace mai mafi girma na kasa Sin, kuma bankin raya muhimman ayyuka na kasar Sin wato China Development Bank ne ya samar da kudaden gudanar da aikin, shugaba Akufo-Addo ya ce, mafi yawan makomar kasar ta dogara ne kan wannan aikin.

Ya ce, idan har kasar Ghana ta yi nasarar sauya fasalin tattalin arzikinta, kuma ta sauya tsarin aikin nomanta zuwa na zamani, tare da samar da kayayyakin da masana'antu ke amfani da su, da kara bunkasa tattalin arzikin kasar, ya ce aikin gina tashar sarrafa iskar gas na Atuabo yana da tasiri mai girma.

Aikin gina tashar sarrafa iskar gas na Atuabo zai iya sarrafa adadin kubik miliyan 120 na iskar gas a kowace rana daga rijiyoyin mai na Jubilee Oil Field, kuma tun daga lokacin da aka kaddamar da fara aikin yana iya sarrafawa da kuma samar da gas da ake amfani da shi a tashar samar da lantarki ta kasar Ghanan. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China