Rahoton ya bayyana cewa, wannan ci gaban ba ya rasa nasaba da yawan mutanen dake amfani da wayoyin salula a kasar Sin. Bayanai na nuna cewa, ya zuwa karshen watan Afrilun wannan shekara, akwai mutane biliyan 1.35 wadanda ke amfani da wayoyin salula a kasar Sin, kuma daga cikin wannan adadi, sama da mutane biliyan 1 suna amfani da intanet.
Rahoton ya kara da cewa, kudaden da aka biya ta na'urorin masu kwakwalwa a cikin kasar ya kai Yuan biliyan11.3, karuwar kaso 8.17 cikin 100 wadda darajarta ta kai kaso 0.14 cikin 100 zuwa Yuan triliyan 658.78.
A cewar wannan rahoto, ya zuwa karshen watan Maris na wannan shekara cibiyoyin kudi na kasar Sin sun bayar da katunan banki biliyan 6.3, wato karuwar kaso 10.7 cikin 100 a kan na shekarar da ta gabata. Yayin da adadin katunan bashi da cibiyoyin suka ba da ya kai miliyan 490.(Ibrahim)