in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya: An fara bincike game da zargin yi wa na'urorin tattara kuri'u kutse
2017-08-10 09:21:05 cri

Hukumar zaben kasar Kenya mai zaman kanta IEBC, ta ce ta fara gudanar da bincike game da zargin yi wa na'urorin

ta na tattara sakamakon zaben kasar kutse.

Da yake tabbatar da hakan, shugaban hukumar Wafula Chebukati ya ce, hukumar na daukar al'amarin da matukar muhimmanci, kasancewar ya shafi 'yancin 'yan kasar na zabar shugaban kasa da suke so.

Chebukati ya ce, hukumarsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen tantance sakamakon kuri'un da 'yan kasar suka kada yadda ya kamata, yana mai fatan nan da kwanaki 5 masu zuwa, za a kai ga tantance daukacin kuri'un mazabu 290 da ake da tababa a kansu, kafin a kai ga fadar sakamakon karshe.

Babban jami'in na IEBC dai ya tabbatar da cewa, sakamakon farko ya nuna shugaba Uhuru Kenyatta ne ke kan gaba da yawan kuri'u a zaben da aka kammala, yayin da kuma babban dan hamayyar sa Raila Odinga, ke zargin wasu sun yi amfani da lambar sirri ta jami'in hukumar zaben da aka hallaka, wajen sauya sakamakon zaben, tare da tabbatar da cewa, shugaban kasar mai ci, ya ci gaba da ba shi tazarar kaso 11 bisa dari na jimillar kuri'un zaben. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China