Al'ummar kasar Kenya kimanin miliyan 19.6 ne suka fara kada kuri'unsu a babban zaben kasar na bana, inda tuni aka bude rumfunan zabe sama da 40,000 a sassan kasar daban daban.
Rahotanni sun tabbatar da bude rumfunan zaben tun da misalin karfe 6 na safiyar Talatar nan, yayin da ake sa ran rufe kada kuri'un da misalin karfe 5 na yamma bisa agogon wurin, in ban da wasu wurare da za a dan kara lokaci idan har akwai bukatar hakan. (Saminu)