in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin Kenya ya hada hannu da UnionPay na kasar Sin domin bunkasa harkokin biyan kudi ta na'ura a gabashin Afrika
2017-08-05 12:27:58 cri
Babban bankin kasuwanci a yankin gabashin Afrika wato bankin kasuwanci na kasar Kenya KCB, ya hada hannu da dandalin bada hidimar hada-hadar kudi na UnionPay a jiya Juma'a domin bunkasa harkokin biyan kudi ta na'ura mai kwakwalwa a gabashin Afrika.

Shugaban sashen aiwatar da tsare -tsare na bankin KCB Dennis Njau, ya ce bisa hadin gwiwar za a fara bada katin cire kudi na UnionPay a gabashin Afrika.

Cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a birnin Nairobi, Dennis Njau ya ce Wadannan katuna za su bada damar biyan kudi ta na'urori masu kwakwalwa ga manya da matsakaita da kananan shaguna, tare da samun damar cin gajiyar hanya mafi sauri ta biyan kudi.

Sakamakon hadin gwiwar, za a fara bada katunan UnionPay mai wani dan karamin na'urar adana bayanai a kasar Kenya, sannan daga bisani a fadada zuwa sauran yankin gabashin Afrika.

Katin na kunshe da karamin na'urar adana bayanai domin gaggauta bada hidima da tsaro da sauki ga abokan huldar bankin.

Dennis Njau ya ce yayin da masu yawon bude ido da harkokin cinikayya ke kara zama kashin bayan tattalin arzikin kasar, hadin gwiwa da UnionPay zai karfafa aikin bankin na bada hidima ga abokan huldarsa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China